Gwamnonin Kudu Maso Kudu Sun Buƙaci Tinubu Ya Soke Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Kudu ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya soke dokar ta-ɓaci da ya ayyana a Jihar Ribas, tana mai cewa babu wata barazana ta tsaro da za ta tabbatar da irin wannan mataki. 

Shugaban ƙungiyar, Gwamna Douye Diri na Bayelsa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba wa shugaban ƙasa damar cire gwamna ba tare da bin matakan doka da aka gindaya a sashe na 188 ba.

Ya ce, “Dokar ta-ɓaci ana ayyanata ne kawai idan akwai yaƙi, farmaki daga waje, barazanar kawo cikas ga zaman lafiya ko kuma bala’in annoba a ƙasa, kamar yadda sashe na 305(3) ya tanada.” 

Gwamna Diri ya ƙara da cewa duk wani rikicin siyasa a Ribas ya kamata a warware shi ta hanyar doka da dimokuraɗiyya, ba wai da ƙarfi ko danniya ba.

Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya janye dokar ta-ɓacin don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da yin kira ga dukkan ɓangarorin da su zauna lafiya da bin dokokin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment