Gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, sun fara ƙoƙarin warware saɓanin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023, domin haɗa kai da farfaɗo da jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.
Wata majiya mai tushe ta bayyana wa Sunday PUNCH cewa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya wakilci gwamnonin PDP a wani taro da suka yi da Wike a Legas, inda suka tattauna kan rikicin siyasa da ke tsakanin Wike da Gwamna Sim Fubara a Jihar Ribas, matsalolin shugabancin shiyyar kudu maso kudu da kuma kujerar Sakataren Jam’iyya na ƙasa da har yanzu ba a warware ba.
Wike ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wasu matsayoyi da Gwamnonin suka ɗauka ba tare da bin dokokin jam’iyya ba, yana mai cewa “duk da ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi, sun ƙara rikita lamarin ne maimakon warwarewa.”
WANI LABARIN: ZIYARAR TINUBU A KATSINA: Bayan Nishaɗi, Kun Gaya Masa Bala’in Da Katsinawan Ƙauye Ke Ciki?
Ya kuma jaddada cewa zai zauna a cikin jam’iyyar PDP muddin za a sake duba waɗannan matsaloli bisa adalci da daidaito, domin samun zaman lafiya da dunƙulewar jam’iyyar.
Makinde, a nasa ɓangaren, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu daga cikin jami’an jam’iyyar ke raina gwamnonin, yana mai cewa “babu wanda ke ƙoƙarin kunyata wani, abin da muke ƙoƙari shi ne a gyara jam’iyyar.”
A cewar wata majiya daga NWC na jam’iyyar, bayan wannan ganawa, Makinde zai sanar da sauran gwamnoni, yayin da Wike zai sanar da magoya bayansa.
Timothy Osadolor, Mataimakin Shugaban Matasa na PDP a matakin ƙasa, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa wannan ganawa da wasu makamanta ta a baya za su taimaka wajen dawo da martabar jam’iyyar, yana mai cewa “APC kamar jirgin ruwa ne da ke cike da kaya fiye da kima, kuma lokaci na dab da kai wa inda jirgin zai nutse.”