Gwamonin Arewa 19 Sun Ziyarci Kaduna, Sun Bayar Da Gudunmawar Kuɗi Ga Mutanen Tudun Biri

Gwamonin Arewa 19 sun haɗu jiya Juma’a a Kaduna domin tattaunawa kan yanda za a magance matsalar tsaro, bunƙasa noma, haƙo mai a yankin Arewa da kuma jajantawa Gwamnan Kaduna Uba Sani kan iftila’in da ya jawo asarar rayuka da dama a Tudun Biri na Ƙaramar Hukumar Igabi da ke jihar.

Taron gwamnonin wanda Gwamna Uba Sani ya sauƙa, shine na farko da suka gabatar tun bayan rantsuwar kama aiki da suka yi a ranar 29 ga watan Mayu na 2023.

Gwamnonin da suka sami halartar zaman sun haɗa da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Yahaya; Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda; mataimakan gwamnonin jihohin Jigawa, Bauchi, Kano, Yobe da Kwara waɗanda suka wakilci gwamnoninsu.

Da yake jawabi ga sauran ƴan’uwansa, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Muhammad Yahaya, ya yi allawadai da hatsarin da ya faru a Tudun Biri, inda ya jaddada cewar akwai buƙatar gwamnonin su sa ƙaimi wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Gwamna Yahaya ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya kan ƙoƙarin da take na magance matsalar tsaro, inda ya ƙara da cewa, akwai buƙatar ƙara ƙaimi daga ɓangaren gwamnonin yankin Arewa domin ganin an kawo ƙarshen garkuwa da mutane, hare-haren ƴanbindiga, rigingimun ƙabilanci da ta’addancin da ya addabi Arewa.

Ya kuma yi alƙawarin ganin cewar ba ai watsi da abun da ya faru a Tudun Biri ba, zasu tabbatar da an yi bincike kuma an biyya diyyar waɗanda abun ya rutsa da su an kuma kare faruwar haka a gaba.

Haka kuma, gwamonin sun bayar da gudunmawar naira miliyan 180 ga waɗanda hatsarin ya rutsa da su, inda suka gabatar da hoton cakin kuɗin ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani.

Tudun Biri
Comments (0)
Add Comment