Haɗakar Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma ta Jigawa, NETJIC, ta ƙaddamar da sabbin shugabanta waɗanda zasu jagorance ta wajen bayar da gudunmawar mutane a gwamnati da kuma yin buɗaɗɗiyar gwamnati a Jigawa.
Haɗakar ta sami gudanar da zaɓen shugabannin ne a zaman da tai jiya Talata a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Zaman ya samu halartar wakilan ƙungiyoyin ci gaban al’umma daban-daban daga faɗin Jihar Jigawa waɗanda suka zaɓi Kwamared Mustapha Umar a matsayin shugaban haɗakar.
Wakilan sun kuma zaɓi Farfesa Usman Haruna a matsayin Sakatare, yayin da suka zaɓi Wada’u Muhd Jahun a matsayin Sakataren Kuɗi, sai kuma Ibrahim Isyaku a matsayin Mai Kula da Harkokin Sadarwa na Haɗakar.
Haka kuma wakilan sun zaɓi Barrister Musa Abubakar Aliyu da Barrister Aisha Suleiman Jahun a matsayin Masu Bayar da Shawara kan Harkokin Shari’a na Haɗakar.
A Karanta Wannan: CIRE TALLAFI: Shawara Ga Gwamnan Jigawa, Namadi
A takaradar da Mai Kula da Harkokin Sadarwa na Haɗakar ta Jihar Jigawa, Ibrahim Isyaku ya rabawa manema labarai, haɗakar ta kuma amince da fitar da wasu muhimman ɓangarori tare da sanya musu jagorori domin samun nasara ƙungiyoyin ci gaban al’umma a jihar.
Muhimman ɓangarorin da jagororinsu sune, Harkokin Lafiya, Musa Mu’azu; Harkokin Ilimi, Tasi’u Abubakar; Kula Da Kuɗaɗen Al’umma, Isah Mustapha; Muhalli, Ahmed Ilallah; Harkokin Gwamnati, Ishaq Hussain Mohd; Bunƙasa Tattalin Arziƙi, Muhd Saudi Shehu; Samar da Abubuwan da Ake Buƙata, Muhd Abdu Dutse; Harkokin Noma, Dr. Ado Nasir; Bunƙasa Harkokin Sadarwa na Zamani, Murtala Lawan Kazaure; Bunƙasa Birane da Manyan Ababen More Rayuwa, Engr. Salisu Kazaure; Cigaban Karkara, Muhd Dodo Malam Madori; da kuma Kare Haƙƙoƙin Zamantakewa wanda Shu’aibu Musa Kafin Gana zai jagoranta.
Sauran sune, Hulɗa da Majalissa, Ayuba Muhammad; Kula da Harkokin Mata, Nafisa Halliru; Samar da Daidaito ga Kowa; Hon. Adamu Shu’aibu Jigawar Tsada; Matasa, Yawan Buɗe Idanu da Wasanni; Hashim Haruna Hashim; Muradun Cigaban Al’umma, Adamu Suleiman; Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, Muhd Musbahu Basirka; da kuma Harkokin Kasuwanci, Ciniki da Sanya Hannun Jari wanda Alhassan Shehu Usman zai jagoranta.
Sabon Shugaban Haɗakar, Mustapha Umar ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban al’ummar Jihar Jigawa da kuma temakawa gwamnati wajen tabbatar da aiwatar da tsare-tsarenta da zasu amfanar da rayuwar talaka.
Ya kuma buƙaci ƴaƴan ƙungiyoyin ci gaban al’umma a Jihar Jigawa a kowanne ɓangare na rayuwa da su bayar da goyon bayansu domin samun cikakkiyar nasarar ƙudire-ƙudiren da aka sa a gaba.