Har Yanzu Maƙiya Ci Gaban Ƙasa Na Yaƙi Da Matatar Dangote

Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa har yanzu yana cikin gagarumin faɗa da ƙoƙari domin kare matatar mansa mai darajar dala biliyan 20 da ke Lekki, Lagos, yana mai cewa “faɗan bai ƙare ba tukuna.”

A wata tattaunawa da ya yi a wani taron masu saka jari a birnin Lagos, Dangote ya ce akwai wasu mutane da suka daɗe suna cin gajiyar tsarin shigo da man fetur na gwamnati da suka haɗe kai don ganin cewa matatar ba ta samu nasara ba.

“Waɗanda suka saba tara kuɗi a cikin shekaru 35 da suka wuce ba za su so nasararka ba idan sun ga ana dakatar da ribarsu,” in ji Dangote, yana mai ƙari da cewa: “Na saba da gwagwarmaya tun ina yaro, kuma zan ci nasara a ƙarshe.”

WANI LABARIN: INEC Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ke Yawo Kan Ci Gaba Da Rijistar Zaɓe

Ya bayyana cewa wasu manyan kamfanonin mai na ƙasashen waje na ƙoƙarin kawo cikas ta hanyar hana matatar samun isasshen ɗanyen mai daga cikin gida, tare da tilasta ta shigo da mai daga ƙasashen waje mai tsananin tsada.

Dangote ya kuma zargi hukumar NMDPRA da bayar da lasisin shigo da man fetur marar inganci da kuma hana matatar sa ta karɓi mai daidai da kasuwa.

Ƙungiyar ƴan kasuwa masu zaman kansu (IPMAN) ta nuna goyon bayanta ga Dangote, inda kakakin kungiyar, Chinedu Udadike, ya ce, “Wannan faɗa ne na kasuwanci, kuma muna tare da shi don kare muradun talakawa.”

A gefe guda kuwa, shugaban ƙungiyar masu sayar da man fetur (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya ce bai kamata a sami rikici a harkar mai ba, yana mai roƙon gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Dangote da sauran matatu suna samun isasshen ɗanyen mai don inganta aikinsu.

Comments (0)
Add Comment