Hauhawar Farashi Ta Mayar Da Karin Albashi Marar Amfani Da Sama Da Kaso 40 Cikin 100

Hauhawar farashi a Najeriya ta mayar da mafi karancin albashi na naira 30,000 a wata a matsayin marar amfani da kaso sama 40 cikin 100 tun daga shekarar 2019 in ji rahoton Afrinvest (West Africa) Limited, kamfanin da ke bayar da shawarwari kan harkokin kudade.

Rahoton mai taken ‘Tsadar Hauhawar Farashi a Kan Matsakaitan Gidaje’, ya bayyana cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata kananan ‘yan kasuwa a Najeriya sun galabaita, yayinda hauhawar farashi tai haifar da mummunan gibi a kan karfin yin siyayyar masu karafin karfi.

Rahoton ya kuma ce, “Alkalumanmu sun nuna cewa, karfin siyan kayan amfani a wajen masu karamin karfi wadanda suka dogara da albashi na mafi karanci naira 30,000 ya ragu matuka zuwa kaso 40.0 cikin 100 tun cikin shekarar 2019 saboda matsatsin hauhawar farashi.

“Mun gano cewa, tun lokacin da aka kara mafi karancin albashi daga naira 18,000 zuwa naira 30,000 a shekarar 2019, hauhawar farashi ta karu daga matakai 68.3 zuwa a 2019 zuwa matakai 517.39 a watan February, 2023.”

Rahoton ya kara da cewa, wannan yanayi ya jefa masu siyen kayayyaki cikin matsanancin hali sama da yanda suka kasance kafin shekarar 2019 da gibin kaso 40.6.

Wadannan bayanai na nuni da cewa, kimar kudaden da masu karamin karfi suke samu a wata ta ragu da kaso 40.6.

A karshe rahoton ya yi nuni da cewar domin magance wannan matsalar, akwai bukatar sake duba mafi karancin albashi tare da yin nagartaccen yunkuri wajen magance hauhawar farashi.

A ‘yan kawanakin da suka gabata ne dai, Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce akwai bukatar Gwamnatin Shugaban Kasa mai Jiran Gado, Bola Ahmad Tinubu da ta duba yiwuwar karin albashi a shekarar 2024 mai zuwa.

AlbashiKarin Albashi
Comments (0)
Add Comment