Hukumar Ci Gaban Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC), wacce aka kafa bisa dokar NWDC Act, 2024 bisa sa hannun Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta sanar da buɗe tsarin karɓar buƙatu domin samun tallafin karatu na ƙasashen waje ga matakin digiri da digiri na biyu da na uku na shekarar 2025/2026.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ƙarƙashin Ma’aikatar Raya Yankunan Ƙasa, an bayyana cewa “an ƙaddamar da wannan tsari ne don tallafa wa matasa masu hazaƙa daga jihohin Arewa maso Yamma wajen samun damar karatu a manyan jami’o’in ƙetare.”
Wannan tallafi ya shafi matakin digiri (undergraduate), digiri na biyu (Master’s) da digiri na uku (PhD) a fannonin Injiniya, Kimiyyar Lafiya, da ICT da Ilimi, inda hukumar ta jaddada cewa “ana buƙatar samun ƙwarewa a fannonin da suka dace don cancanta da samun gurbin.”
A cikin ƙa’idojin cancantar, hukumar ta ce “dole ne ɗalibi ya kasance ɗan asalin ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto ko Zamfara,” kuma ya samu sakamako mai kyau na credit biyar a matakin WAEC/NECO (ciki har da Turanci, Lissafi, da Kimiyya) ga masu neman digiri.
WANI LABARIN: APC Ta Amince Da Gwamna Namadi A Matsayin Ɗan Takararta Tilo A Zaɓen Gwamnan Jigawa Na 2027
Ga masu neman Master’s, kuwa, sai sun samu Second Class Upper, yayin da masu neman PhD za su buƙaci CGPA na ƙalla 4.00 a Master’s da suka kammala.
“Dole ne masu neman tallafin su cika fom ɗin da ke kan shafin [www.nwdc.gov.ng/scholarships](http://www.nwdc.gov.ng/scholarships), kuma ba a biyan kuɗin komai wajen cike buƙatar,” in ji hukumar.
A ƙarshe, hukumar ta lissafa takardun da ake buƙata da suka haɗa da: CV, takardun makarantar firamare da sakandare, shedar haihuwa, shedar asalin gari daga ƙaramar hukuma da jiha, fasfo, NYSC ko takardar yafe hidimar kasa, takardun digiri, sakamakon WAEC/NECO, takardar bayanin son yin karatu (Letter of Motivation) da kuma official transcript.
Za a fara karɓar buƙatun a ranar 5 ga Mayu, 2025, kuma ana iya tura tambayoyi kai tsaye ta imel: [scholarships@nwdc.gov.ng](mailto:scholarships@nwdc.gov.ng) domin neman ƙarin bayani.