Hukumar FBI da ta hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta DEA a Amurka sun roƙi kotun tarayya da ke birnin Washington D.C. da ta ba su ƙarin kwanaki 90 domin kammala bincikensu kan batun da ya shafi zargin safarar miyagun kwayoyi da aka danganta da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda aka ce ya faru a birnin Chicago a shekarun 1990.
Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoto da aka miƙa wa kotu a matsayin “Joint Status Report” tsakanin FBI, DEA da mai ƙarar, Aaron Greenspan, wanda ya ce ya gabatar da buƙatarsa ne domin samun cikakken bayani daga hukumomin bisa dokar ƴancin samun bayanai (FOIA).
Greenspan, wanda ya kafa dandalin PlainSite, ya ƙi amincewa da buƙatar ƙarin kwanaki 90, yana mai cewa, “ya kamata a kawo takardun da aka riga aka gano nan da mako mai zuwa, ko a ƙalla a gabatar da kwafinsu ba tare da cire wani ɓangare ba, sannan a kammala gabatar da sauran cikin kwanaki 14.”
KARANTA WANNAN: Wani Gwamna Ya Musanta Jita-Jitar Komawarsa Jam’iyyar APC, Ya Ce “Ina Nan A PDP Har Abada”
Kotun, ƙarƙashin alƙalinta Beryl Howell, ta umarci FBI da DEA tun farko da su ba da matsayin bincikensu zuwa ranar 2 ga Mayu, 2025, kan buƙatun da Greenspan ya miƙa tsakanin 2022 zuwa 2023.
Hukumar FBI da DEA sun fara bincikensu bisa buƙatu masu lamba FBI Nos. 1588244-000 da 1593615-000 da kuma DEA Nos. 22-00892-F da 24-00201-F, inda suka bayyana cewa suna buƙatar ƙarin lokaci domin tantance wasu takardun.
Greenspan ya bayyana niyyarsa na neman a biya shi kuɗaɗen da ya kashe wajen shari’ar da suka haɗa da $402 na kuɗin shigar da ƙara da kuma $38.22 na aika wasiƙu, jimilla $440.22.
Yayin da FBI da DEA ke neman ƙarin lokaci har zuwa 31 ga Yuli domin kawo cikakken rahoto, Greenspan yana buƙatar hakan ya kasance a ranar 31 ga Mayu, yana mai jaddada cewa an samu jinkiri da yawa da hukumomin suka jawo tun bayan fara shari’ar.