Daga: Captain Yobe
Hukumar dake shirya kwallon yashi ta Najeriya (NBSL) ta kulla yarjejeniyar hadingwiwa da kamfanin ƙera motoci na Nijeriya, Innoson Motors, kamfani na farko a Najeriya dake ƙera motoci a fadin ƙasar.
Sanarwar kulla yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin aka je zagaye na biyu na gasar kwallon yashin ta ƙasa ta 2024 da ake gudanarwa a birnin Nnewi, na jihar Anambra.
An yi haɗingwiwar ne domin tabbatar da kawo ci gaba da ɗabbaƙa wasan tun daga tushe.
Shugaban Kamfanin Innoson Motors, Cif Innocent Ifedaso Chukwuma wanda ya halarci wurin bikin buɗe gasar, ya bayyana irin son da yake yi wa wasan, ya kuma tabbatar da cewa zai ba da dukkanin irin gudunmawar da ake buƙata domin kawo ci gaba.
Ana sa bangaren shugaban Hukumar Kwallon Yashi ta Afrika, Mahmud Hadejia ya bayyana cewa sun yi hadin gwiwar ne domin tabbatar da ci gaban wasan kwallon yashi.
“Haɗin gwiwar shine domin tabbatar da cigaban wasan, tare da baiwa ƴan Nijeriya dama”, in ji Hadejia.