Hukumar NiMet Ta Bayyana Yanda Yanayi Zai Kasance Daga Lahadi Zuwa Talata A Najeriya

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta fitar da rahoton hasashen yanayi daga ranar Lahadi har zuwa Talata, inda ta bayyana cewa za a fuskanci rana, gajimare da kuma yiwuwar ruwan sama da hadari a sassa daban-daban na Najeriya, musamman yankin arewa da kudu.

A cikin rahoton da ta fitar a Abuja a ranar Asabar, NiMet ta bayyana cewa ranar Lahadi za ta kasance da rana mai ƙarfi a yawancin jihohin arewa, sai dai ana sa ran samun gajimare da hadarin ruwan sama a wasu sassan jihohin Gombe, Bauchi, Kaduna, Taraba da Adamawa da rana ko da yamma.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa a yankin tsakiyar Najeriya kamar Kwara, Plateau, Nasarawa, Niger, Benue da Kogi, akwai yiyuwar samun hadari da ruwan sama da yamma.

Ga yankin kudu kuma, NiMet ta ce ana sa ran samun ruwan sama da hadari tun daga safiya a jihohin Cross River, Lagos, Ogun, Bayelsa, Rivers, Delta da Akwa Ibom, yayin da wasu sassan za su sake fuskantar ruwan sama a yammacin ranar.

“A ranar Litinin, hasken rana mai ɗumi da ƴan gajimarai za su mamaye yawancin jihohin arewa, sai dai akwai yiyuwar ruwan sama da hadari da safe a wasu sassan Taraba da Adamawa,” in ji rahoton.

WANI LABARIN: Bayan Karɓar Maƙudan Kuɗin Fansa, Ƴan Bindiga Sun Halaka Wani Shugaban APC

Sannan, akwai yiwuwar samun ruwan sama da hadari da yamma a jihohin Kaduna da Taraba, wanda ke nuna ci gaba da samun hazo da guguwa a cikin kwanakinnan.

A yankin tsakiyar ƙasar kuma, za a sami hasken rana da gajimare da safe, tare da yiwuwar samun ruwan sama da hadari da yamma a Nasarawa, Kogi da Benue.

A yankin kudu maso kudu da kudu maso yamma, akwai yiwuwar ruwan sama da hadari da safe da yamma, musamman a jihohin Rivers, Delta, Ondo, Oyo da Edo.

NiMet ta shawarci manoma, ma’aikata da mazauna yankunan da su lura da hasashen kuma su guji tafiya a lokacin da ruwan sama mai ƙarfi ke sauƙa domin kauce wa hatsari.

Rahoton ya kuma nuna damuwa dangane da yawan ambaliya da za a iya fuskanta, musamman a yankunan da ke da ƙarancin tsayayyen tsari na magudanar ruwa.

Shugabannin yankuna da hukumomin lafiya an shawarce su da su ƙara kulawa da matakan kariya domin rage hatsarin da ka iya faruwa a wannan lokacin.

Comments (0)
Add Comment