IBTILA’IN GOBARAR MAJIYA: Ayoyin Tambaya A Kan Nijeriya Kasa Dayace?

Daga: Ahmed Ilallah

Tabbas bala’in da ya faru a sanadiyar gobarar Tankar Fetur a garin Majiya da ke Karamar Hukumar Taura a Jahar Jigawa, ya tadawa mutane da yawa hankali, ba kawai al’umar Jihar Jigawa ba, har ma kasa baki daya dama sauran mutanen duniya.

Kusan wannan hadari da asarar rayukan da ya jawo ya kasance wanda ba a taba yin irinsa ba a fadin Nijeriya.

Wannan gobara ta jawo sandiyar rauwar mutane kimanin 200, wasu ma har yanzu suna kwance a asibitoci a na sama musu lafiya.

Gwamnatin tarayya, ta aiko tawaga don jajantawa mutanen jahar Jigawa. Hakazalika gwamnonin Arewacin Nijeriya karkashin kungiyar su, sun kawo irin wannan ziyara ta ta’aziyya, har ma da bada gudunmawar kudade, dama sauran manyan mutane sun kawo irin wannan ta’aziyya da bayar da tasu gudunmawa.

Amma ayar tambayar anan shine; ina mutanen Kudancin Nijeriya? Ina Gwamnonin Kudancin Nijeriya? Ina Manayan Yan Siyasar Kudancin Nijeriya? Wajen yiwa mutanen Jigawa Jaje a kan wannan iftila’in?

Wannan batu ya tuna min wasu kalaman Tsohon Shugaba Kasarnan Chief Olusegun Obasanjo na wannan makon yayin da Kungiyar su Tsohon Gwamnan Kano Malam Shekarau suka kai masa.

Shugaban ya nuna takaicin sa da yan Nijeriya suka fi danaganta kansu da yanki da kula da yankunan su, maimakon sanya kasar Nijeriya guda daya a gaba.

Har a wannan lokacin a iya nawa bibiyar, har yanzu banga wani gwamna da ga kudancin Nijeriya ya zo Jigawa ba domin yi musu jaje da ta’aziyya, ko kuma turo wa da wakilci don jajantawa mutanen Jigawa a matsayin yanuwa yan Nijeriya da suka samu wannan ibtala’in.

Rashin nuna damuwa da ma yiwa junanmu jaje da taimako a yayin irin wannan bala’I, wanda kawai kowa yana ganin mutanen yankinsa ne, kawai nasa, ko da su kawai zaiyi mu’amala irin wannan, tabbas a kwai tasgaro a hadin kan al’uumar Nijeriya.

Kullum shugaban siyasa a Nijeriya basa nuna dayantakar Nijeriya sai a lokacin da suke nemen shugabancin Nijeriya, wanda wannan ba karamin nuna kishin kasa bane, da ma nunawa yan baya kishin kasa da daukan duk dan kasa a kan dan uwa koda kuwa daga wane yanki yake.

Irin wannan halin ko in kula da kuma kin nuna siyasar yan uwantaka a tsakanin yan Nijeriya kan iya kara kiyayya da kiki juna a tsakanin yan Nijeriya.

Ba karamin kuskure bane a ce a kwai wata jaha a wannna kasa da za su ki jajantawa mutanen Jigawa ba a kan wannan ibtila’i.

Ahmad Ilallah
Comments (0)
Add Comment