IMF Ta Buƙaci Najeriya Ta Ƙarawa Ƴan Ƙasa Haraji, Ta Kuma Inganta Tsarin Kasafin Kuɗi Don Rage Talauci

Hukumar IMF ta ce Najeriya tana buƙatar ƙara samun kuɗaɗen shiga daga cikin gida, da inganta tsarin kasafin kuɗi, tare da faɗaɗa tsarin tallafin kuɗi domin fitar da miliyoyin ‘yan ƙasa daga kangin talauci, duk da cewa akwai alamun ci gaba daga sauye-sauyen tattalin arzikin da aka soma tun 2023.

A cewar sabon rahoton nazarin tattalin arziƙin Najeriya na 2025 da hukumar ta fitar, Najeriya ta ɗauki matakan gyara kan manyan matsaloli da suka daɗe suna hana cigaba, kamar batun tallafin man fetur, matsalolin musayar kuɗi da raunin tsarin kuɗin gwamnati.

Hukumar ta yabawa sauye-sauyen da suka dawo da samun amincewar masu saka hannun jari, da ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen waje, amma ta ce hauhawar farashi, talauci da matsalolin wutar lantarki na ci gaba da hana ainihin ci gaban da ake buƙata.

WANI LABARIN: JISEPA Ta Kama Lalatattun Kayayyakin Da Darajarsu Ta Haura Naira Miliyan 14 A Jigawa

“Inganta ci gaban tattalin arziƙi ga kowa da kowa na buƙatar faɗaɗa tsarin tallafin kuɗi da ake dashi yanzu haka,” in ji IMF.

Hukumar ta bayyana cewa tsakanin 2014 da 2023, adadin GDP na ƴan ƙasa ya samu matsakaiciyar raguwa, inda kashi 42 cikin 100 na al’umma ke rayuwa cikin matsanancin talauci.

Tana mai cewa mafi yawan kuɗaɗen shiga na tafiya wajen biyan bashi, abin da ke hana zuba jari a fannin walwalar jama’a da gine-gine, inda ta ce “aikace-aikace masu tasiri suna buƙatar kasafin da ya dace da gaskiya da bayyananniyar gudanarwa.”

IMF ta ƙara da cewa dole ne gwamnati ta ƙara tsaurara manufofin kuɗi domin rage hauhawar farashi, da kuma tabbatar da zaman lafiyar tattalin arziƙi.

Comments (0)
Add Comment