A Ɗauki Nauyin Karatun Mace 100% Ko Kuma . . .

‘Ya mace, idan ba za a iya ɗaukar nauyin karatunta da buƙatunta a lokacin karatu 100% ba, a haƙura, ya fi maslaha da alheri.

Ke ma idan kin san gidanku ba za su ba ki full scholarship ba, ki haƙura.

Wasu na amfani da talaucinsu yara mata su ɓata ‘ya’yan mutane. Yaran mata suna zama ƙananan karuwai a manyan makaranta, don kwaɗayin mallakar manyan wayoyi, sutura mai tsada, lafiyayyen abinci… wasu kuma su faɗa shaye-shaye.

Idan babu halin ba wa yarinya scholarship ta tafi university ko college, sai ta riƙa zuwa Islamiyya ko wata part-time ta kusa, ta kuma koyi sana’ar da za ta riƙa yi a gida. Idan kuma ta sami miji, ta yi aure.

Allah ya wadata mu daga falalarsa,

Allah ya shiryar mana da zuri’a.

Ilimin Mata
Comments (0)
Add Comment