INEC Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ke Yawo Kan Ci Gaba Da Rijistar Zaɓe

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta sanya ranar 27 ga Mayu, 2025 a matsayin ranar da za a ci gaba da yin Rijistar Zaɓe da sauran ayyukan da suka shafi canja wurin rijista da sake katin zaɓe ga waɗanda nasu ya ɓata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban hukumar, Rotimi Oyekanmi, ya fitar ta dandalin X a ranar Lahadi, hukumar ta bayyana cewa labarin da ke yawo ba shi da tushe balle makama, kuma jama’a su yi watsi da shi.

“Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na son sanar da al’umma cewa ba ta fitar da wata sanarwa ba kan komawa aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a ko kuma maye gurbin katunan da suka ɓace,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da bin hanyoyinta na gargaɗi da bayar da sanarwa ta kafafenta na hukuma idan lokaci ya yi da za a kammala shirye-shiryen komawa aikin rijistar.

WANI LABARIN: Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Yamma Ta Buɗe Ƙofar Karɓar Buƙatun Tallafin Karatu Don Fita Waje

“Jama’a su watsar da wannan ƙarya da ke yawo cikin jama’a musamman a yanar gizo, wadda ba ta da sahihanci kuma ba daga hukumar ya fito ba,” kamar yadda INEC ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “lokacin da hukumar za ta fara sabuwar rijistar masu kaɗa ƙuri’a da sauran ayyuka, za ta sanar da cikakken bayani ta kafafen sadarwa na hukuma.”

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke nuna damuwa kan yadda ba a sake buɗe rijistar ba, yayin da ake samun matsin lambar ganin an fara tun kafin zaɓukan 2027.

Comments (0)
Add Comment