INEC Ta Bayyana Adadin Waɗanda Su Kai Rijistar Farko A Awanni 7 Bayan Fara Sabuwar Rijistar Katin Zaɓe

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa mutane 69,376 sun yi pre-registration a cikin awanni bakwai bayan buɗe shafin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR), inda Sam Olumekun ya ce “shafin ya fara aiki da 8:30 na safe ya kuma kuma samu rajistoci 69,376 zuwa 3:30 na yamma.”

Ƙididdiga ta nuna maza 33,803 ne (48.7%), mata 35,573 (51.3%), tare da matasa masu shekaru 18–34 su 48,033 (69.2%), alamar ƙarfin sha’awar shiga tsarin neman yin zaɓe.

“Shafin yana aiki sa’o’i 24 a kowace rana a adireshin https://cvr.inecnigeria.org, in ji hukumar, tana mai ƙari da cewa za a fara rajistar kai tsaye a ofisoshi 811 na jiha da ƙananan hukumomi daga ranar Litinin 25 Agusta 2025, da 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma a ranakun aiki, kuma “nema ta internet da ta kai tsaye za su gudana tare” tare da bayyana rahoton mako-mako.

INEC ta tunatar da cewa an buɗe rajistar ne ga ƴan ƙasa ƴan shekara 18 zuwa sama kawai, inda ta gargaɗi masu “rajista sau biyu” a matsayin laifi, amma “ana ba da damar canjin mazaɓa (inter/intra-State) da maye gurbin katin zaɓe da ya ɓace ko ya lalace” a lokacin rijistar.

Comments (0)
Add Comment