INEC Zata Ƙarasa Zaɓuɓɓuka Da Gudanar Da Zaɓen Cike Gurabe A Watan Fabarairu Na 2024

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce zata gudanar da ƙarasa zaɓuɓɓuka da zaɓuɓɓukan cike gurbi a duk faɗin Najeriya a satin farko na watan Fabarairu, 2024, domin cike gurabe a majalissun jihohi da na tarayya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana hakan a zaman tattaunawa da shugabannin jam’iyyu gabanin zaɓuɓɓuka wanda aka gudanar a Abuja, yau Litinin.

Za a ƙarasa zaɓuɓɓuka ne ga jam’iyyu da ƴan takarkarun da suka shiga babban zaɓen da ya gabata, sai dai idan an samu jam’iyyun da suke nufin canja ƴantakarar da suka rasu.

Su kuma ƙarasa zaɓuɓɓuka za a yi su ne sabbi a guraren da ake da buƙatar hakan.

Farfesa Yakubu ya bayyana cewar, a ƙarshen sauraron ƙararrakin zaɓe, kotuna sun umarci hukumar INEC da ta ƙarasa zaɓuɓɓuka a mazaɓu 34 na tarayya da na jihohi, waɗanda suka haɗa da mazaɓar sanata guda 1, mazaɓun ƴan majalissar tarayya guda 11 da kuma mazaɓun jihohi guda 22.

Ya bayyana cewar za a gudanar da dukkanin zaɓuɓɓukan ne a rana ɗaya, inda ya ce dole jam’iyyu su gudanar da zaɓuɓɓukan cikin gida a inda ake buƙatar hakan bisa tanadin doka kuma a lokacin da dokar ta ware.

INEC
Comments (0)
Add Comment