Injiniyoyi Daga Rasha Sun Isa Kamfanin Tama Da Ƙarafa Na Ajaokuta

Wata tawagar ƴan gaba mai ɗauke da ƴan Ƙasar Rasha su ashirin da uku, sun isa Kamfanin Sarrafa Tama da Ƙarafa na Ajaokuta domin domin yin nazari kan yanayin kamfanin.

Ƴan Ƙasar Rashan waɗanda da ma sune suka fara aikin samar da kamfanin sama da shekaru arba’in da suka wuce, sun je kamfanin ne da injiniyoyi a ƙoƙarin da ake na kammala aikin samar da kamfanin.

An bayyana cewar, za a sauya waɗansu daga cikin injinan da aka dasa a kamfanin da irin na zamanin yanzu domin samun sauƙin aiyukan kamfanin.

Shugaban Riƙo na kamfanin, Suma’ila Abdul-Akaba wanda ya tabbatar da zuwan injiniyoyin ga NTA, ya ce, tawagar ta ziyarci sassan kamfanin da dama domin tantance abubuwan da ake buƙata don cigaba da aikin.

Kamfanin Ajaokuta
Comments (0)
Add Comment