Iya Masu NIN Number Ne Zasu Mori Sayen Shinkafa Kan Farashin Naira 40,000

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kawai mutanen da ke da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa ta NIN ne za su samu damar sayen buhun shinkafa mai nauyin 50kg a farashin N40, 000 a matsayin wani bangare na tallafin abinci ga ƴan Najeriya.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ta hannun Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce shirin sayar da shinkafar zai kasance ne bisa tsarin “mutum ɗaya buhu ɗaya” a lokacin ƙaddamar da shirin.

Kyari ya bayyana cewa farashin buhun shinkafar zai kasance N40,000 kacal a matsayin tallafi daga gwamnati don rage raɗaɗin matsalar abinci da ke fuskantar ƙasa.

Ya ce wannan tallafin abincin ya zo a daidai lokacin da kasar ke cikin ƙalubale, don haka ya yi kira ga ƴan kasa da su yaba da wannan yunƙuri na gwamnati.

An sanya wata tawagar gwamnati domin tabbatar da gaskiya da adalci a rabon shinkafar, inda za a tabbatar da wanda ya cancanta ne kaɗai ta amfani da NIN da lambar waya yayin da ma’aikatan Gwamnatin Tarayya zasu yi amfani da lambar IPPIS.

Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya su bada haɗin kai ga jami’an gwamnati domin tabbatar da nasarar shirin, yana mai fatan farashin shinkafa zai ragu tare da sauran kayan abinci a dalilin shirin.

Tsadar Rayuwa
Comments (0)
Add Comment