JAMB Ta Gano Ɗalibai 21 Da Ke Da Sakamakon Jarabawar Bogi

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta gano ɗalibai 21 da suka yi amfani da sakamakon jarrabawar Interim Joint Matriculation Board (IJMB) na bogi don samun gurbin karatu a shekarar 2023.

Wata takarda daga JAMB ta bayyana cewa, Jami’ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) ce ta bankaɗo dalibai 12 daga cikin waɗanda suka gabatar da sakamakon bogin.

JAMB ta jaddada buƙatar duba takardun shaidar ɗalibai kafin a yi musu rajista, kuma ta jaddada cewa dukkan takardun dole ne su kasance da sa hannun wanda ke da alhakin sanya hannu.

Hukumar, wadda ke zama mai kula da jarrabawar IJMB da JUPEB, ta bayyana cewa tana ɗaukar matakai don magance matsalar sakamakon bogi da kuma hana faruwar hakan a nan gaba.

Wannan matsala ta biyo bayan binciken da Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC ta gudanar a kan rashin daidaito a sakamakon jarabawa, wanda ya ƙara jaddada buƙatar tsauraran matakan tantancewa.

JAMB
Comments (0)
Add Comment