JAMB Zata Hana Wasu Manyan Makarantu Ɗaukar Sabbin Ɗalibai

Hukumar JAMB ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da ɗaukar ɗalibai na shekarar karatu ta 2024 da 2025 ba ga kowace makaranta da ta ƙi tura jerin sunayen sabbin ɗaliban da ta ɗauka.

Wannan matakin, wanda ya samo asali daga umarnin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, na nufin daƙile ɗaukar ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba.

A taron da aka yi da jami’an kula da ɗaukar ɗalibai, Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce, “Duk makarantar da ba ta tura jerin sunayen shekarar 2022 da 2023 ba, ba za a amince mata da ɗaukar ɗalibai na shekarar 2024 da 2025 ba.”

Ya bayyana cewa an yi sassauci na wucin gadi saboda wasu makarantu na kammala ɗaukar dalibai, amma nan gaba dole su bi doka.

Kakakin JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya tabbatar cewa, za fallasa jerin sunayen waɗanda suka karya wannan doka a jaridu.

Comments (0)
Add Comment