Jami’an Immigration Sun Ki Aikinsu, Suna Shirin Shiga Zanga-Zanga Kan Rashin Biyansu Alawuns Na Aikin Zabe

Wasu daga shugabannin Nigeria Immigration Service (NIS) yanzu haka suna shirya gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu kudaden alawuns na aiyukan zaben da ya gabata kamar yanda SaharaReporters ta gano.

Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar ne lokaci guda a duk shalkwatocin hukumar na dukkan jihohin Najeriya.

Majiyoyi masu yawa sun tabbatarwa da SaharaReporters cewa da dama daga jami’an hukumar sun yi watsi da aikinsu.

“Da yawanmu suna cikin fushi cewar har yanzu ba a biya mu alwuns na aikin zaben shugaban kasa da ‘yan majalissun tarayya wanda aka kammala ba,” in ji wani jami’in hukumar da yai magana da SaharaReporters.

“Ba a biya mu alawuns dinmu ba a daidai wannan lokaci, sannan kuma wadanda suka fusatan daga jami’an namu sun shirya gudanar da zanga-zanga.”

Wani jami’in na immigration ya ce, “Jami’an Immigration na shirin  gudanar da zanga-zanga da yajin aiki saboda rashin biyan alwuns na zabe, CG na immigration yana dab da yin ritaya, sannan kuma yana son ya gudu da kudadenmu.”

Wani jami’in kuma ya ce, “Hukumar Immigration ta ki biyan mu alawuns na zabe, duk da cewar sauran hukumomi sun biya jami’ansu.”

“Da yawanmu sun biya kudin dakin hotel ne a lokacin aikin zaben da ya gabata, amma abin da kawai muke ji shine ana shirye-shiryenn biyanmu.

ImmigrationZanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment