Jam’iyyun Adawa Sun Fara Shirye-Shiryen Samar Da Haɗaka Don Ƙalubalantar Tinubu A 2027 

Wasu ƙungiyoyin siyasa na adawa sun fara ƙoƙarin kafa abin da suka kira “Haɗakar Ƴan Adawa Mafi Girma” don kifar da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027. 

Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, wanda ke wakiltar mazaɓar Ideato a Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa jam’iyyun adawa za su kafa ƙungiyar ƙarfafa kai, ko da ba tare da PDP ba. 

Otunba Segun Showunmi, tsohon mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ne ya ƙaddamar da ƙungiyar National Opposition Movement Coalition (NOMC), wacce ake kira ‘The Alternative’ ko kuma ‘Mafita’ a Hausa. 

Ya bayyana wannan matakin a matsayin wata hanya ta farfaɗo da dimokuraɗiyya tare da ƙarfafa masu adawa. 

Ƙungiyar haɗakar jam’iyyu ta Coalition of United Political Parties (CUPP) ta amince da wannan tsari tare da alƙawarin haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki don samar da ƙarfin da zai iya ƙalubalantar APC, yayin da Chief Chekwas Okorie, wanda ya kafa jam’iyyar APGA, ya yi hasashen cewa za a samu sauyin tsarin siyasa daga yanzu zuwa tsakiyar shekarar 2025. 

“PDP Ta Gaza A Matsayin Jam’iyyar Adawa” – Ugochinyere 

Da yake magana a Akokwa, Jihar Imo, Ugochinyere ya soki shugabancin PDP ƙarƙashin Ambassador Umar Damagum, yana mai zarginsa da cewa yana taimakawa wajen raunana jam’iyyar. 

Ya yi kira da a gudanar da “yaƙin ƙarshe” don ceto PDP da dawo da ita matsayin jam’iyyar adawa mai ƙarfi. 

“Mun fara tattara ƙarfafa. Idan dattawanmu ba za su tashi su ƙalubalanci wannan matsala ba, mu za mu tashi,” in ji shi. 

Showunmi Ya Ƙaddamar da NOMC Don Kare Dimokuraɗiyyar Najeriya 

A lokacin ƙaddamar da NOMC a Abuja, Showunmi ya nuna damuwa kan lalacewar tsarin zaɓe, rashin aƙida a cikin jam’iyyun siyasa, da kuma raguwar amincewar masu zaɓe da tsarin dimokuraɗiyya. 

Ya bayyana cewa wannan ƙungiyar ba jam’iyyar siyasa ba ce, sai dai wata hanyar samar da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki don dawo da amincewa ga tsarin dimokuraɗiyya. 

CUPP da NCFront Sun Goyi Bayan Samar da Haɗakar

Sakataren CUPP na ƙasa, Chief Peter Ameh, ya bayyana goyon bayansa ga wannan haɗaka, yana mai cewa tana da muhimmanci wajen kawar da “mulkin cin hanci da rashawa” na APC tare da tabbatar da kyakkyawan shugabanci. 

Hakazalika, mai magana da yawun NCFront, Mallam Hamisu Santuraki, ya bayyana cewa suna kan gaba wajen shirya gagarumin motsi na siyasa wanda zai haɗa ƴan adawa daga jam’iyyun siyasa daban-daban. 

Jam’iyyar Labour ta Buƙaci Samun Matsayi mai Ƙarfi a Haɗakar

Mai magana da yawun Jam’iyyar Labour, Obiora Ifoh, ya bayyana fata kan damar jam’iyyar a 2027, yana kira ga ƴan Najeriya da su goyi bayan haɗin gwiwa na ƴan adawa don kawo sauyi mai kyau ga shugabanci. 

Comments (0)
Add Comment