JANYE TALLAFI: Ƙaramar Hukumar Haɗejia Ta Ragewa Matafiya Kuɗin Hawa Mota

A yayin da ake tsaka da kokawa kan tsadar sufuri a faɗin Najeriya, Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta NURTW, reshen Ƙaramar Hukumar Haɗejia dake Jihar Jigawa, ta sanar da ragin kuɗin motar layukan Kano da Gumel.

Shugaban Kungiyar Alhaji Sabo Innani ne ya sanar da rage kuɗin motar a ranar Laraba da ta gabata, cikin wata tattaunawarsa da gidan rediyo Sawaba a garin Haɗejia.

Ya ce Hadejia zuwa Kano, da ake biyan naira 2,800 a baya, a yanzu an rage kuɗin ya koma naira 2,500.  Sai kuma Haɗejia zuwa Gumel da ake biyan naira 1,300, an rage ya koma naira 1,200, ya ƙara da cewa akwai sauran hanyoyin da za a duba waɗanda zasu biyo baya

Labari Mai Alaƙa: JANYE TALLAFI: Jihohin Borno, Adamawa Da Yobe Sun Sauƙaƙawa Ma’aikata, Manoma Da Ɗalibai Kuɗin Hawa Mota

Shugaban ya ce wannan ragi ya zo ne bayan Shugabankaramar Hukumar Haɗejia, Hon. Abdulkadir Umar Bala ya roƙi ƙungiyar ta nemi hanyar sassauatawa matafiya tsadar sufuri, a wani bangare na ragewa al’umma raɗaɗin janye tallafin man fetur, yayin wata ganawa da yayi da shugabancin ƙungiyar direbobin a sakatariyar Karamar Hukumar.

Tsadar sufuri dai ta ƙara ƙamari a Najeriya tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa kujerar shubancin Najeriya maraba da zuwa da janye tallafin man fetur a Najeriya.

HadejiaJanye Tallafin MaiTsadar Sufuri
Comments (0)
Add Comment