JANYE TALLAFI: Yau Zanga-Zangar Ƴan Ƙwadago Ta Fara, Ma’aikatan Ma’aikatun Mai Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Zaman tattaunawa na kwanaki biyu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago bai kai ga cimma komai ba har zuwa yammacin jiya Talata, yayinda Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, da Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, suka gama shiri domin fara zanga-zangar nuna rashin goyon baya ga tsarin janyen tallafin man fetur a Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikatan ma’aikatun mai ƙarƙashin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Ma’aikatun Sarrafa Fetur da Iskar Gas suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a jiya Talata, inda suka bayyana rashin tausayin da ake nuna musu daga ɓangaren Ma’aikatar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa, wadda ke ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya.

Ana zaton zanga-zangar da yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon suka tsunduma a yau kan janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi zai iya tsayar da komai a ƙasar ya kuma durƙusar da tattalin arziƙi.

Su dai ma’aikatan ma’aikatun man fetur tun a jiya ne suka fara zanga-zangar, inda suka rufe ofishin Ma’aikatar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa na Lagos tare da yin alƙawarin rufe sauran ofisoshin da ke faɗin Najeriya.

Da yake magana kan yajin aikin da aka fara a yau a jiya Talata, Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce ƙungiyar ba ta da wani dalili na janye zanga-zanga da yajin aikin da ta shirya shiga a yau.

Ajaero ya yi wannan maganar ne ƴan awanni bayan wani zaman na Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Rage Raɗaɗi wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa, Aso Rock Villa da ke Abuja, wanda bai kai ga cimma komai ba.

Ajaero ya nuna cewar, an samu nasarar kiran mutane na su fito su goyi bayan zanga-zangar da yajin aikin, kuma mutane sun amsa kiran.

A ƙoƙarinta na magance shiga zanga-zangar da yajin aikin, Gwamnatin Tarayya ta gana da shugabannin ƙungiyoyin NLC da TUC a ranar Litinin da ta gabata, to amma ganawar ta gaza samar da sasanto tsakanin ɓangarorin biyu.

A baya dai wata kotu ta dakatar da shugabannin ƙwadagon daga shiga yajin aiki bayan Gwamnatin Tarayya ta buƙaci kotun ta yi hakan.

Da yake magana jim kaɗan bayan ganawa da wakilan Gwamnatin Tarayya, Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja ya ce ƙungiyar zata duba roƙon gwamnati na a samu maslaha cikin lalama, to amma, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Biyu, Titus Amba ya ce babu wata sabuwar matsaya da aka samu tun bayan jawabin da shugaban ƙasa ya yi wa ƴan ƙasa a ranar Litinin da yamma, don haka zanga-zanga tana nan.

Gwamnatin TarayyaNLCTUCYajin AikiZanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment