A safiyar Talata tsohuwar tauraruwa e Kannywood, Mansura Isa ta sanar da rasuwar ta shfaubtavna Facebook.
Mansura, wadda ta yi addu’ar samun rahama da Fati Slow ta ce marigayiyar ta rasu ne da daddare a kasar Habasha, kuma a can za a yi jana’izarta.
Ta ce, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
“Allah Ya yi wa Fati Slow rasuwa jiya da daddare a Habasha kusa da Sudan.
“A can za a yi jana’izarta, amma ana zaman makoki a gidansu da ke Unguwar Uku.”
Fati Slow Motion tana daga cikin jaruman Kannywood da suka yi tashe a shekarun 2000.
A baya-bayan nan Fati Slow Motion ta yi tashe a kafofin sada zumunta, saboda amfani da kalmomi ‘Kebura’ da kuma ‘No body is Fafet’.
AMINIYA