Sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai fara aiki ba tare da sanyin jiki ba don tabbatar da nasarar jam’iyyar mai mulki a zaɓukan gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Imo da Kogi da kuma Bayelsa.
Tsohon gwamnan Kano, Ganduje ya yi wannan jawabi ne jim kaɗan bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban APC na ƙasa a yau Alhamis.
Ganduje ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, kuma ya yi alƙawarin cewa a zamanin mulkinsa zai tabbatar da ganin demokaraɗiyya ta yi tasiri a cikin gida.
Ya kuma yi alƙawarin cewa zai tabbatar da rijistar gaskiya ta ƴaƴan jam’iyyar APC, kuma zai mayar da hankali ga sha’anin gudanar da zaɓe da kuma sulhunta rikice-rikicen jam’iyyar.
A cewarsa, sabon shugabancinsa zai samar da yanayi na bai ɗaya ga dukkan ƴaƴan jam’iyyar a lokacin zaɓukan fitar da gwani.