Kwamitin bayar da muƙamin SAN (LPPC) ya amince da ɗaukaka lauyoyi 57 zuwa matsayin Senior Advocate of Nigeria (SAN) a wani zama da aka gudanar a Abuja.
An samu lauyoyi 56 daga ɓangaren shari’a kai tsaye da guda ɗaya daga ɓangaren ilimi, wato Farfesa Chima Ubanyionwu.
Matan da aka ɗaukaka sun haɗa da Mrs Oyinkan Badejo-Okusanya da Mrs Chinyere Ekene Moneme, waɗanda su ne kaɗai mata da aka karrama a bana.
Sauran sun haɗa da Antoni Janar na Abia Ikechukwu Uwanna da Antoni Janar na Osun Oluwole Jimi-Bada, da Labaran Magaji na Nasarawa.
WANI LABARIN: Dole Ne Sai Ɗalibi Ya Kai Shekaru 12 Kafin Ya Shiga Ƙaramar Sikandire A Najeriya
“Matsayin SAN na nuni ne da ƙwarewa da gagarumar gudunmawa a ɓangaren shari’a ko ilimi,” in ji kwamitin.
Za a gudanar da bikin rantsar da sababbin SAN-SAN ɗin a ranar 29 ga Satumba, 2025 a gaban Babbar Mai Shari’a ta Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun.
Kwamitin ya ce duk waɗanda aka zaɓa dole su halarci wani taron horarwa kafin a rantsar da su daidai da umarnin BOSAN.
Ga jerin sunayen:
- Theophilus Kolawole Esan, Esq
- Fedude Zimughan, Esq
- Ernest Chikwendu Ikejle, Esq
- Victor Esiri Akpoguma, Esq
- Leslie Akujuobi Njemanze, Esq
- Akintunde Wilson Adewale, Esq
- Preye Agedah, Esq
- Omamuzo Erebe, Esq
- Hannibal Egbe Uwaifo, Esq
- Olumide Ekisola, Esq
- George Ejie Ukaegbu, Esq
- Oromena Justice Ajakpovi, Esq
- Tairu Adebayo, Esq
- Bawa Akhimie Osali Ibrahim, Esq
- Suleh Umar, Esq
- Emeka Akabogu, Esq
- Godwin Sunday Ogboji, Esq
- Godwin Aimuagbonrie Idiagbonya, Esq
- Adeolu Olusegun Salako, Esq
- Adetunji Oso, Esq
- Achinike Godwin William-Wobodo, Esq
- Shuaib Agbarere Mustapha, Esq
- Adizua Chu-Chu Okoroafor, Esq
- Olanrewaju Tasleem Akinsola, Esq
- Amaechi Fidelis Iteshi, Esq
- Adakole Edwin Inegedu, Esq
- Oyinkansola Badejo-Okunsanya, Esq
- David Ogenyi Ogebe, Esq
- Aminu Sani Gadanya, Esq
- Oluseun Awonuga Adentyi, Esq
- Ikechukwu Raphael Uwanna, Esq
- Ayodeji Joseph Ademola, Esq
- Kelechi Nwaiwu, Esq
- Lawal Garba Hudu, Esq
- Ibim Simeon Dokubo, Esq
- Luka Abubakar Haruna Musa, Esq
- Shakeer Adedayo Oshodi, Esq
- Oluwole Tolulope Jimi-Bada, Esq
- Mubarak Tijani Adekilekun, Esq
- Chinyere Ekene Moneme, Esq
- Shuaibu Magaji Labaran, Esq
- Kingsley Tochukwu Udeh, Esq
- Augustine Enenche Audu, Esq
- Ali Dussah Zubairu, Esq
- Adeyemi Adebambo Pitan, Esq
- Habeeb Abdulrahman Oredola, Esq
- Abdulakeem Labi-Lawal, Esq
- Victor Agunzi, Esq
- Nkwegu Luke Ogbagaegwu, Esq
- Bidemi Ifedunni Ademola-Bello, Esq
- Temilolu Femi Adamolekun, Esq
- Abdulkarim Kabiru Maude, Esq
- Adedayo Gbolahan Adesina, Esq
- Usman Yusuf Zaiyanu, Esq
- Taiwo Azeez Hassan, Esq
- Olufemi Olubummi Oyewole, Esq
- Prof. Chima Josephat Ubanyionwu