JERIN SUNAYE: Sojojin Da Suka Mutu Sanadiyar Harbo Jirginsu Da Ƴan-ta’adda Suka Yi A Neja

Sojojin Najeriya sun yi jana’izar sojojin da suka rasa rayukansu a sanadiyar hatsarin jirginsu da ƴan-ta’adda suka jawo da kuma waɗanda aka kai harin kwanton ɓauna.

A makon da ya gabata ne, sojojin Najeriya suka bayyana cewar jami’ansu 36 suka rasa rayukansu a sanadiyyar hatsarin jirgin da ya faru a yankin Chukuba na Shiroro da kuma harin ƴan-ta’addan da ya faru a kan titin Zungeru-Tegina duk a Jihar Neja.

A yau Juma’a ne Rundunar Sojojin Najeriya ta binne sojojin a wani taro na bankwana da kuma girmamawa da ta shirya saboda marigayan, wanda ya samu halartar Ministan Tsaro, Badaru Abubakar; Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da kuma Hafsan Hafsoshi, Janar Christopher Musa.

KARANTA WANNAN: Sojojin Najeriya Da Na Birtaniya Za Su Yi Aiki Tare Wajen Kawo Ƙarshen Boko Haram – Badaru

Sauran manyan mutanen da suka halarci jana’izar sojojin sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, Hafsan Sojojin Ƙasa, Lt.-Gen. Taoreed Lagbaja; Hafsan Sojojin Ruwa, Emmanuel Ogalla; dangin marigayan da abokanansu na arziƙi da kuma sauran jama’a.

Ga jerin sunayen sojoji 22 da muƙamansu daga marigayan:

  1. MARIGAYI MAJOR SEGUN ABIODUN ONI (N/14427)
  2. MARIGAYI FLIGHT LIEUTENANT ALFRED ANTHONY DURYUMSU (NAF/4481)
  3. MARIGAYI FLIGHT LIEUTENANT IBRAHIM ABUBAKAR ADAMU (NAF/4521)
  4. MARIGAYI LIEUTENANT GBENGA MICHAEL ODUSAMI (N/17314)
  5. MARIGAYI LIEUTENANT USMAN SHEHU ALKALI (N/18250)
  6. MARIGAYI 02NA/51/512 SERGEANT FAROUK MOHAMMED
  7. MARIGAYI 03NA/53/2083 CORPORAL IBRAHIM GARBA
  8. MARIGAYI 09NA/64/4275 CORPORAL CHIROMA POGUYAMTA
  9. MARIGAYI 11NA/66/10694 CORPORAL ADAMA ISSAC
  10. MARIGAYI 11NA/66/11292 CORPORAL HARUNA JAMILU
  11. MARIGAYI 12NA/68/5890 CORPORAL SAMAILA BASHIRU
  12. MARIGAYI ABLE REGULATOR SULEIMAN MAHMUD KAILANI OFFICIAL NUMBER-X14168
  13. MARIGAYI NAF19/35900 CORPORAL JAURO AMOS
  14. MARIGAYI 12NA/68/5192 LANCE CORPORAL SUNDAY OKOPI
  15. MARIGAYI 13NA/70/3552 LANCE CORPORAL EKPEYONG EDET
  16. MARIGAYI NAF13/28034 LANCE CORPORAL ALARIBE DANIEL NNAMDI
  17. MARIGAYI NAF14/28578 LCPL BRIGGS STEPHEN
  18. MARIGAYI 16NA/75/1484 LANCE CORPORAL YAKUBU AYUBA
  19. MARIGAYI 16NA/75/4442 LANCE CORPORAL NURA MOHAMMED
  20. MARIGAYI 20NA/79/4397 PRIVATE HABIB ALIYU
  21. MARIGAYI 20NA/79/4412 PRIVATE TANKO WAJE
  22. MARIGAYI NAF17/33175 AIR CRAFTMAN ABUBAKAR ABDULRAHAMAN
Matsalar Tsaro
Comments (0)
Add Comment