Sojojin Najeriya sun yi jana’izar sojojin da suka rasa rayukansu a sanadiyar hatsarin jirginsu da ƴan-ta’adda suka jawo da kuma waɗanda aka kai harin kwanton ɓauna.
A makon da ya gabata ne, sojojin Najeriya suka bayyana cewar jami’ansu 36 suka rasa rayukansu a sanadiyyar hatsarin jirgin da ya faru a yankin Chukuba na Shiroro da kuma harin ƴan-ta’addan da ya faru a kan titin Zungeru-Tegina duk a Jihar Neja.
A yau Juma’a ne Rundunar Sojojin Najeriya ta binne sojojin a wani taro na bankwana da kuma girmamawa da ta shirya saboda marigayan, wanda ya samu halartar Ministan Tsaro, Badaru Abubakar; Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da kuma Hafsan Hafsoshi, Janar Christopher Musa.
KARANTA WANNAN: Sojojin Najeriya Da Na Birtaniya Za Su Yi Aiki Tare Wajen Kawo Ƙarshen Boko Haram – Badaru
Sauran manyan mutanen da suka halarci jana’izar sojojin sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, Hafsan Sojojin Ƙasa, Lt.-Gen. Taoreed Lagbaja; Hafsan Sojojin Ruwa, Emmanuel Ogalla; dangin marigayan da abokanansu na arziƙi da kuma sauran jama’a.
Ga jerin sunayen sojoji 22 da muƙamansu daga marigayan:
- MARIGAYI MAJOR SEGUN ABIODUN ONI (N/14427)
- MARIGAYI FLIGHT LIEUTENANT ALFRED ANTHONY DURYUMSU (NAF/4481)
- MARIGAYI FLIGHT LIEUTENANT IBRAHIM ABUBAKAR ADAMU (NAF/4521)
- MARIGAYI LIEUTENANT GBENGA MICHAEL ODUSAMI (N/17314)
- MARIGAYI LIEUTENANT USMAN SHEHU ALKALI (N/18250)
- MARIGAYI 02NA/51/512 SERGEANT FAROUK MOHAMMED
- MARIGAYI 03NA/53/2083 CORPORAL IBRAHIM GARBA
- MARIGAYI 09NA/64/4275 CORPORAL CHIROMA POGUYAMTA
- MARIGAYI 11NA/66/10694 CORPORAL ADAMA ISSAC
- MARIGAYI 11NA/66/11292 CORPORAL HARUNA JAMILU
- MARIGAYI 12NA/68/5890 CORPORAL SAMAILA BASHIRU
- MARIGAYI ABLE REGULATOR SULEIMAN MAHMUD KAILANI OFFICIAL NUMBER-X14168
- MARIGAYI NAF19/35900 CORPORAL JAURO AMOS
- MARIGAYI 12NA/68/5192 LANCE CORPORAL SUNDAY OKOPI
- MARIGAYI 13NA/70/3552 LANCE CORPORAL EKPEYONG EDET
- MARIGAYI NAF13/28034 LANCE CORPORAL ALARIBE DANIEL NNAMDI
- MARIGAYI NAF14/28578 LCPL BRIGGS STEPHEN
- MARIGAYI 16NA/75/1484 LANCE CORPORAL YAKUBU AYUBA
- MARIGAYI 16NA/75/4442 LANCE CORPORAL NURA MOHAMMED
- MARIGAYI 20NA/79/4397 PRIVATE HABIB ALIYU
- MARIGAYI 20NA/79/4412 PRIVATE TANKO WAJE
- MARIGAYI NAF17/33175 AIR CRAFTMAN ABUBAKAR ABDULRAHAMAN