Gwamnatin Jihar Jigawa tare da UNICEF sun ƙaddamar da atisayen horaswa ga fiye da jami’ai 90 kan Result-Based Budgeting wato kasafin kuɗi mai amfani a Katsina, da mayar da hankali kan inganta kuɗaɗen ɓangaren ilimi.
A cewar Muntaka Mukhtar na ofishin UNICEF na Kano, “muna son mu tallafa wa gwamnati ta samu kuɗaɗen da suka isa, masu inganci, da adalci, bayyanannu kuma waɗanda za a iya bibiya don ɓangeren ilimi,” tare da jaddada cewa “mu kuma tabbatar gwamnati na iya duba adadin da ke zuwa ga kowanne yaro, ta kuma yi nazari kan amfaninsa.”
Ya ce manufar ita ce kawar da manyan ƙalubalai biyu – “yawan yara da ba sa zuwa makaranta” da kuma “yara na aji amma ba sa iya koyon komai,” ta hanyar tabbatar da duk kuɗi ya yi amfani ga sakamakon yara.
Ɗaya daga cikin masu bayar da horon, Vahyala Kwaga, ya ce ana so “a ga aiwatar da ƙa’idoji da dabarun da aka koya a ayyukan yau da kullum, wata-wata da shekara-shekara” domin a sami sabuwar hanya ta gudanar da kuɗin jama’a da inganta ilimi.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Matakin Farko ta Jigawa, Baffa Abubakar, ya ja hankalin mahalartan da su zamo masu amfani da abun da suka koya, yana mai cewa “ku tabbata kun yi amfani da abin da kuka koya, ku ƙirƙiri hanyar sadarwa wadda za ta daidaita aikinku da kasafin kuɗi.”