JIGAWA: Gwamna Namadi Ya Kori Mai Ba Shi Shawara Kan Majalisar Tarayya Ya Janye Masa Dukkan Alfarma

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya tsige Mai Ba shi Shawara kan Harkokin Majalisar Tarayya, Rabi’u Garba Kaugama, kuma matakin ya fara aiki nan take a cewar sanarwar Ofishin Sakataran Gwamnati, Bala Ibrahim.

A cewar sanarwar, “da wannan ci gaban, an janye dukkan haƙƙoƙi da gata da suka shafi ofishinsa na Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Majalisar Tarayya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “an umarci tsohon Mai Ba da Shawarar da ya gaggauta miƙa dukkan dukiyar gwamnati da ke hannunsa ga Ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Jigawa.”

Ba a bayyana dalilin tsigewar ba, lamarin da ya ƙara tayar da jijiyar wuya a siyasar cikin gida yayin da ake jiran a bayyana wanda zai maye gurbin kujerar.

Masu lura da al’amura na ganin matakin na nuna irin tsauraran ƙa’idojin mulkin da gwamnan ke ɗauka da nufin daidaita tafiyar gwamnati kafin babban ƙalubalen siyasa na gaba.

Comments (0)
Add Comment