JIGAWA: Gwamnati Na Shirin Sauya Tsarin Tsangaya Don Samar Da Ingantacciyar Jiha

Jihar Jigawa ta kammala taron dabarun aiki na kwana biyu ga Hukumar Tsangaya (JSTEB) a Global Luxury Suites, Kano, inda aka gina tubalin sabuwar tafiyar da za ta sauya tsarin almajirci.

A cewar shirin gwamnatin jihar, wannan aikin “ya yi daidai kai tsaye da Manufofin Gwamna 12” da ke fifita ci gaban gina ɗan Adam da juyin juya halin ilimi.

Mohammed T. Mohammed, Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Tsangaya, ya bayyana cewa “ina matuƙar alfahari da halartar wannan taro,” inda aka haɗa manyan jami’an gwamnati, mambobin hukumar, ƙungiyar Alarammomi, CSO, NGO, CBO da sauran masu ruwa da tsaki.

An ayyana taken shirin a fili a matsayin “Sauya Tsangaya Don Samar da Ingantacciyar Jihar Jigawa” (“Transforming Tsangaya Education for a Prosperous Jigawa State”).

Tare da goyon bayan PLANE, mahalarta sun tsara manyan abubuwan bai wa fifiko, tsarin aiwatarwa, hanyoyin sa ido da ɗorewar kuɗi domin “tsarin ya dace da buƙatun ilimi, tattalin arziƙi da zamantakewa ba tare da barin addini da al’ada su salwanta ba.”

An yaba da yadda aka shirya taron cikin tsari da haɗin kai, “inda aka nuna cikakken daidaito, tsari da sadaukarwa daga dukkan ɓangarori.”

A ƙarshe an miƙa godiya ga Gwamna bisa jagoranci mai hangen nesa, “domin wannan mataki shi ne gina sabuwar gada da ke mayar da Tsangaya ɓangare mai ƙarfi a tsarin ilimin Jigawa.”

Comments (0)
Add Comment