JIGAWA: Jihar Na Neman Zama Babbar Cibiyar Samar Da Abinci Ta Najeriya – Dr. Saifullahi

Jihar Jigawa na ƙoƙarin zama babbar cibiyar abinci ta Najeriya, inda Gwamna Umar Namadi ya ƙaddamar da shirin juyin tsarin noma domin ƙaruwar shinkafar da ake nomawa, amfani da zamani a aikin gona, da rage illar ambaliya.

Ƙwararren Mai ba da Shawara kan Noma, Dr Saifullahi Umar, ya bayyana cewa jihar na da kadada miliyan 2.4 ta ƙasa, inda kadada miliyan 1.9 ta dace da noma.

A cewarsa, “muna na biyu a samar da shinkafa a Najeriya, muna na ɗaya a samar da alkama, kuma muna kan gaba a riɗi da zoɓo da gero, dawa da wake.”

Ya ce Jigawa na samar da tan miliyan 2 zuwa miliyan 2.5 na shinkafa a shekara amma ana ƙoƙarin kaiwa tan miliyan 3.6, kimanin kashi 35 cikin 100 na buƙatar Najeriya, tare da manufar, “mu rage shigo da kaya, mu kare ayyukan yi, mu ƙarfafa tsaron abinci.”

Don cimma wannan buri, an kafa kamfanin kayan aikin gona, wato Mechanisation Service Company haɗin gwiwar dala miliyan 16 da ya kawo taraktoci 300, injinan girbi 60, boom sprayers 150 da injinan samar da irin shinkafa 150 domin ƙara saurin aiki da rage asara.

Shirin ya ƙunshi faɗaɗa hanyoyin ban-ruwa, gyaran dam guda 10, da amfani da kwarin Kogin Mayo mai kimanin kilomita 200 domin noma a ko’ina cikin shekara, tare da aikin yasar koguna, gina jinga da shirye-shiryen samar da inshorar amfanin gona.

“Mun yashe koguna, mun gina fiye da kilomita 70 na jinga, mun saka manoman shinkafa 23,000 cikin shirin inshora da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jiha,” in ji Saifullahi, yana mai cewa canje-canjen za su sa Jigawa ta ciyar da kanta kuma ta taimaka wajen tsaron abincin a Najeriya baki ɗaya.

Comments (0)
Add Comment