JIGAWA: Jihar Ta Ƙaddamar Da Babban Shirin Gyaran Ilimi, An Ware Naira Biliyan 8 Don Mayar Jami’ar Khadija Ta Ilimin Likitanci

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙaddamar da sauye-sauyen ilimi masu faɗi domin faɗaɗa samun shiga manyan makarantu, inganta gine-gine, da haɗa sana’o’i da karatun boko, a cewar Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isa Yusuf Chamo a wata tattaunawa da PUNCH a Dutse.

Farfesa Isa ya ce an fara shirin ne bayan cikakken binciken buƙatun da ake da su, wato NEEDS Assessment, wanda ya gano giɓin da ke addabar manyan makarantu a jihar.

A cewarsa, “daga cikin matakan farko mun ƙara yawan kuɗin da ake bai wa manyan makarantu, bursary, da kashi 200 cikin 100 don rage nauyin kuɗi ga iyalai,” matakin da ya ƙara damar ƙaruwar masu shiga manyan makarantun jihar guda bakwai.

Game da tallafi, ya bayyana cewa jihar na kashe fiye da Naira biliyan 12 a shekara, biliyan 5 na waje da sama da biliyan 7 a cikin gida, tare da magance matsalar da ɗalibai 184 da rikicin Sudan ya hana karatu ta hanyar mayar da su jami’o’in Cyprus, inda gwamnati ta biya sufuri, masauki da inshorar lafiya.

Ya ƙara da cewa, “mun ɓullo da Damodi Student Care Initiative” domin ƙwato yaran karkara da suka fita ko ba su taɓa shiga makaranta ba, kuma “ilimin mata daga firamare zuwa jami’a yanzu kyauta ne a Jigawa.”

A kan gine-gine, an zuba biliyoyi wajen sabunta kayayyaki, ciki har da aikin Naira biliyan 6 na gina Faculty of Medicine da ɗakunan kwana 480 ga mata a Jami’ar Sule Lamido, Kafin Hausa, tare da sababbin ɗakunan kwana, bayar da bita da samar da ajujuwa a Polytechnic Dutse, JSIIT Kazaure da sauran kwalejoji; an kuma sayi Khadija University kan Naira biliyan 11 da ware mata Naira biliyan 8 don mayar da ita Jami’ar Kiwon Lafiya ta Musamman don rage kuɗin tura ɗalibai ƙasashen waje. Ya ce gwamnatin ta ware Naira biliyan 15 a bana ga sana’o’i da injuna a ɓangaren makarantun sakandare tare da kafa cibiyoyin samun hazaƙa huɗu ciki har da babban wajen bita na Naira biliyan 5 a Dutse, sannan “dukkan kwasa-kwasai na da amincewar hukumomin da suka dace,” kuma ana daidaita matsayin HND da digiri kamar yadda umarnin tarayya ya tanada.

DalibaiIlimiJami'aJigawaMata
Comments (0)
Add Comment