Gwamnatin Jihar Jigawa ta ɗauki nauyin ɗalibai 184 don su ci gaba da karatun likitanci a Near East University, Cyprus, wasu kuma za su koma Integral University a India kamar yanda rahoton GREEK CITY TIMES ya nuna.
Jami’an gwamnatin jihar sun bayyana shirin a matsayin wani ɓangare na ‘ajandar raya ɗan Adam’ da ke nufin magance ƙarancin likitoci ƙwararru musamman mata a faɗin jihar.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun yi wa manema labarai bayani a filin jirgi yayin komawarsu daga hutu, inda Nura Illiyasu ya ce, “muna godiya ga Mai girma (gwamna), ya ɗauki nauyin tikitin jirgi, abinci da sauran kuɗaɗe; ba don wannan tallafi ba, da bai yiwu mu dawo hutu mu kuma koma karatu ba.”
Wani ɗalibi, Yusuf Murtala, ya bayyana shirin a matsayin “ya fi ƙarfin tallafi,” yana mai cewa, “ba mu da matsala da makaranta ko da tallafin gwamnati, komai na tafiya lafiya, mun gode wa gwamna da ma’aikatar ilimi.”
Sakataren Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Jihar, Sa’idu Magaji, ya ce gwamnati ta saki fiye da Naira biliyan 4.1 don kuɗin makaranta da alawus na ɗaliban, tare da amincewa da Naira miliyan 6.7 na tikitin komawa ga ɗaliban Jigawa da ke India.
Ya ƙara da cewa an rattaba hannu kan yarjeniyoyi da jami’o’i tare da yarjejeniyar bond da ke tilasta wa ɗaliban su dawo su yi wa jihar aiki daidai da shekarun da suka shafe a makaranta, yana mai cewa, “manufar ita ce gina ƙarfin ɗan’adam; ana buɗe asibitoci sabbi, muna buƙatar ƙwararrun likitoci su cika su.”
Magaji ya ce shirin na cikin ajandar ci gaba mai ƙudiri 12 na jihar, kuma baya ga yawancin ɗaliban likitanci akwai kimanin wasu fannonin 15, ciki har da waɗanda aka fito da su daga yakin Sudan, da suke karɓar tallafi.