JIGAWA: Majalisar Tarayya Ta Yaba Wa Jihar Kan Juyin Juya Halin Lafiya

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ayyukan Lafiya ya yaba da zuba jari da gyare-gyaren Jigawa a ɓangaren lafiya.

Shugaban kwamitin, Amos Magaji, ya ce “fiye da kashi 15% na kasafin jihar na ɓangaren samar da lafiyar jama’a,” kuma hakan ya canja yanayin da ake ciki a baya.

Ya taya Gwamna Umar Namadi murnar lashe kyautar dala 500,000 na PSC Leadership Challenge a fannin kiwon lafiya.

Magaji ya kuma yabawa daidaita albashin ma’aikatan lafiyar jihar da na Tarayya, yana mai cewa “inda wasu na barin ƙasa, anan mutane na shigowa ne don amfanar da al’umma.”

Gwamnan ya ce “lafiya ita ce tubalin ilimi da tattalin arziƙi,” yana jaddada ƙarfafa asibitocin kula da lafiya na matakin farko.

Ya bayyana shirin “medical village” mai ɗauke da cibiyar gwaje-gwaje, cibiyar kula da zuciya da masana’antar iskar oxygen domin rage yawon neman magani.

Ya ce ziyarar ta kara musu kwarin gwiwa don cimma shimfidar inshorar lafiya ga kowa a Jigawa tare da hadin kai da Majalisa.

Comments (0)
Add Comment