Jigawa SUBEB Na Iya Karɓar Shirin Tsarin Karatun MuKaranta Don Koyon Karatu Da Rubutu A Jihar

Daga Mika’il Tsoho, Dutse

Hukumar Ilimi a Matakin Farko ta Jihar Jigawa, SUBEB, na iya haɗa shirin MuKaranta na karatun Hausa domin bunƙasa manhajar makarantun firamare.

Wannan bayanin ya fito ne daga Shugaban Hukumar ta SUBEB, Farfesa Haruna Musa, yayin wani taron tantancewa da ya gudana na rana ɗaya, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Kamfanin MuKaranta Literacy Resources Limited da Bono Energy, a ranar Talata a Tahir Guest Palace da ke Dutse.

Farfesa Haruna Musa ya nuna jin daɗinsa game da shirin, inda ya bayyana cewa shirin ya inganta basirar yara sosai, inda yake ba su damar koyon karatu da rubutu cikin sauƙi.

“Muna tattaunawa da su kan yanda za a tabbatar da ci gaba da shirin tare da faɗaɗa shi zuwa ƙarin ƙananan hukumomi, saboda ya yi tasiri sosai a kan ɗalibanmu,” in ji shi.

Da yake magana kan ƙalubalen da shirin ke fuskanta, shugaban ya yi kira ga iyaye mata da Kwamitin Gudanar da Makarantu (SBMC) da su ɗauki nauyin kula da makarantun, saboda gwamnati na yin duk mai yiwuwa don samar da duk kayan koyo da koyarwa da ake buƙata.

Ya kuma yabawa Kamfanin MuKaranta Literacy Resources Limited da Bono Energy bisa ƙoƙarinsu, inda ya ƙarfafa wa mutane guiwa kan su yi koyi da su don inganta ilimi a Jihar Jigawa.

A nasa jawabin, Jami’in Shirye-shiryen MuKaranta na Jihar, Malam Bashir Yakubu, ya bayyana cewa shirin ya inganta basirar ɗalibai wajen gane haruffa, inda aka samu ƙaruwa daga kashi 2% zuwa 92% cikin wata goma sha takwas da aka gudanar da shirin.

Ya kuma ƙara da cewa an gabatar da Shirin MuKaranta a makarantu 198, inda ɗalibai sama da 22,500 suka amfana a cikin tsawon watanni goma sha takwas da aka yi da shirin a jihar.

Malam Yakubu ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Jihar Jigawa da masu bayar da tallafi kan yiwuwar tsawaita lokacin gudanar da shirin.

Jihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment