Jigawa Ta Nemi Haɗin Gwiwar EFCC Wajen Yaƙar Cin Hanci Da Rashawa

Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa (PCACC) ta nemi haɗin gwiwa da Hukumar EFCC domin inganta bincike da daƙile cin hanci a jihar.

Shugaban PCACC, Salisu Abdu, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da suka kai hedikwatar EFCC a Abuja ranar Alhamis, 6 ga Fabrairu, 2025.

Ya ce hukumarsu sabuwa ce, don haka suna buƙatar horo da jagoranci daga EFCC domin inganta aikinsu.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba da shirin haɗin gwiwar, yana mai cewa hakan zai rage nauyin EFCC a matakin jiha.

Ya buƙaci hukumar ta Jigawa da ta dage wajen kare gaskiya da kauce wa siyasa a aikinta.

Ya kuma shawarce su da su mayar da hankali wajen daƙile satar kuɗaɗen gwamnati da bunƙasa kuɗin shiga na cikin gida (IGR) a jihar Jigawa, domin amfanin al’ummar jihar.

Comments (0)
Add Comment