Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana shirin gina ƙananan dam guda 10 a faɗin jihar domin inganta noman rani da kuma rage haɗarin ambaliya a yankunan karkara.
Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin rigakafin ambaliya da sauyin yanayi, Hamza Hadejia, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a gidan rediyon Jigawa a Dutse, jiya Juma’a.
Hadejia ya ce, “Za mu gina waɗannan dam ne a wuraren da ruwa ke ratsawa don hana ambaliya da kuma kare gonaki daga mamayewar ruwan damina.”
Ya kara da cewa, ana gudanar da bincike don tantance wuraren da suka fi dacewa da gina dam ɗin, domin tabbatar da inganci da kuma amfanin su ga manoma.
“Idan muka gina waɗannan dam, za su taimaka matuƙa wajen haɓaka noma a lokacin rani, inda manoma za su samu isasshen ruwa don shuka amfanin gonarsu,” in ji shi.
Shirin yana daya daga cikin matakan gwamnatin jihar na inganta tattalin arziƙin jama’a ta hanyar samar da ingantaccen ruwan ban-ruwa ga manoma, wanda hakan zai haɓaka amfanin gona da inganta rayuwar al’umma.
Ya kuma yabawa gwamnan jihar bisa wannan tsari da aka fito da shi domin tallafawa manoma da rage wahalhalun da suke fuskanta sakamakon sauyin yanayi da ambaliya.
Gwamnatin ta yi alƙawarin cewa za a fara aiwatar da wannan aiki nan bada jimawa ba, domin tabbatar da cewa manoman jihar sun fara amfana da shi kafin ƙarshen shekarar nan.