Jihar Kaduna Ta Fara Gina Babban Birni Mai Gidaje Dubu 500,000 Don Talakawa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara gina babban birni mai ɗauke da gidaje 500,000 don talakawa da marassa ƙarfi mazauna jihar.

Wannan babban birni dai, gwamnatin za ta gina shi ne, haɗin guiwa da kamfanin ƙasar Qatar mai suna Qatar Construction Company ƙarƙashin shirin ƙasar Qatar na Sanabil Project.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yabawa Ofishin Jakadancin Qatar da kuma shirin Sanabil Project bisa samar da wannan dama da bunƙasa tattalin arziƙi da kuma zaɓar Kaduna a matsayin wajen da za a yi wannan babban aikin domin amfanar talakawa.

KARANTA WANNAN: Tallafin Naira Biliyan Biyar Ba Zai Magance Talauci Ba, In Ji NLC

Da yake bayani kan shirin samar da sabon birnin, Uba Sani ya ce, wannan aikin zai samar da ababen more rayuwa ingantattu tare da mayar da Kaduna wurin kwatance wajen samun gidaje isassu kuma masu araha da kuma samun ingantaccen tsaro da nutsuwa domin gudanar da kasuwanci.

Ya ƙara da cewar, wannan sabon birni, zai kuma samar da damarmakin kasuwanci ga ƴan kasuwar ƙasashen waje, sannan kuma zai amfani ƴan kasuwar cikin gida tare da bunƙasa tattalin arziƙi.

Gwamnan ya kuma ce, a sabon birnin, za a samar da gidaje ne ga talakawa, za a kuma samar da wuraren shan magani, shaguna, gonakin noman kaji, gonakin noman damuna da na rani.

Da yake magana kan shirin samar da birnin, Jakadan Ƙasar Qatar a Najeriya, Dr. Ali Bin Ghanem Al-Hajri ya bayyana cewar haɗin kansa wajen ganin samun nasarar aikin, ya kuma ce, ƙasar Qatar ta yi alƙawarin yin aiyukan tallafawa al’umma a Jihar Kaduna domin amfanin talakawa.

Jihar Kaduna
Comments (0)
Add Comment