Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatarwa da masu neman Jihar Tiga da Jihar Gari daga cikin Jihar Kano cewar, Majalissar Tarayya za tai musu adalci a lokacin gyaran kundin tsarin mulki.
Sanata Barau ya bayar da wannan tabbaci ne a lokacin da mambobin kwamitin neman jihohin ƙarƙashin jagorancin, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, suka kai masa ziyara a Majalissar Tarayya a jiya Laraba.
Sanatan wanda shine shugaban Kwamitin Majalissar Dattawa kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki ya ce, Malissar ta 10 zata bai wa duk wasu mutane masu neman a ƙirƙira musu jiha cikakkiyar dama domin su gabatar da buƙatunsu.
Ya yabawa ƴan kwamitin neman jihohin Tiga da Gari bisa juriyar da suka nuna tsawon shekaru suna neman jihohin.
Tun da farko dai, Sanata Doguwa ya nuna matuƙar buƙatar da ake da ita na cire sabbin jihohi biyu daga Jihar Kano.
Ya ce, a shekaru 40 da suka gabata, suna ta neman a raba Jihar Kano duba da girmanta da yawan mutanenta domin samar da ingantaccen ci gaban al’ummar guraren.
“Muna son ƙarin jihohi daga Jihar Kano ta yanzu. Wannan zai kawo gagarumin ci gaban da ake buƙata. A shekaru 40 da suka gabata, muna ta neman a ƙirƙiri ƙarin jihohin biyu a Kano. Ba wai muna neman hakan ba ne domin mu yi faɗa da wani, a a, sai dai don a gaggauta samun ci gaba,” in ji shi.