Jihohi 16 Da Suka Ƙi Aiwatar Da Dokar Ƙarin Shekarun Ritaya Ga Malaman Makaranta

Shekaru huɗu bayan rattaba hannu kan dokar ƙarin shekarar ritayar malaman makaranta zuwa 65 a duniya ko bayan shekaru 40 na aiki, rahoto ya bayyana cewa jihohi 16 a Najeriya sun ƙi aiwatar da wannan doka har kawo yanzu.

Dokar da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ita a shekarar 2021 ta tanadi sabuwar ƙa’ida wadda ta cire malamai daga ƙa’idar ritaya ta shekarun haihuwa 60 ko aiki na shekaru 35.

Jihohin da su ƙi aiwatarwar sun haɗa da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Ekiti, Gombe, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kwara, Lagos, Niger, Ogun, Oyo, Rivers da Sokoto, kamar yadda rahoton Ƙungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) ya tabbatar.

WANI LABARIN: Gwamna Namadi Ya Shigar Da Ƴan Siyasa Cikin Tsarin Inshorar Lafiya Na Jigawa

Ƙungiyar Malaman Sakandare (ASUSS) ta bayyana damuwa da rashin aiwatar da dokar, tana mai cewa hakan yana tauye haƙƙin malamai da gurɓata manufar dokar tarayya.

A wata sanarwa, shugabannin ƙungiyar sun ce: “Hanya mafi kyau ta tunawa da marigayi Shugaba Buhari ita ce aiwatar da wannan doka a ko’ina cikin ƙasar domin girmama gudummawar da ya bayar ga harkar ilimi.”

Comments (0)
Add Comment