Jihohi da Yawan Masu Nema: Masu Neman Aiki Miliyan 1.91 Na Rige-Rigen Samun Aikin Para-Military A Najeriya

Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta bayyana cewa sama da masu neman aiki miliyan 1.91 ne suka yi rajista don neman guraben aiki a hukumomin tsaro na para-military a wannan shekarar.

Wannan bayani ya fito ne daga shafin yanar gizon hukumar a ranar Litinin, inda aka tabbatar da cewa kafin fara neman aikin, an shaida cewa aƙalla mutane dubu 30,000 ne za a ɗauka gaba ɗaya.

Bisa ga alƙaluma, jihar Kogi ce ta fi yawan masu nema da mutum 116,243, sai Kaduna da Benue da suka samu 114,599 da 110,644 bi da bi.

Sauran sun haɗa da Kano 89,421; Neja 79,567; Kwara 78,467; Katsina 76,917; Nasarawa 76,677; Adamawa 68,381; Oyo 67,255 da Plateau 63,450.

Akwai kuma Osun 62,399; Borno 56,955; Ondo 53,963; Akwa Ibom 52,531; Bauchi 52,159 da Imo 48,301.

Jihar da ta fi ƙarancin masu nema ita ce Bayelsa mai mutane 11,680 kacal, yayin da Lagos ta samu 14,221.

Hukumar ta ce “za a tuntuɓi waɗanda aka zaɓa nan gaba kaɗan tare da bada ƙarin bayani kan yanda abubuwan zasu kasance.”

Ta kuma shawarci masu nema da su “rinƙa bibiyar saƙonnin email da na waya a makonnin da ke tafe domin duba sabuwar sanarwa.”

Wannan yawan masu nema ya sake jaddada tsananin buƙatar aiki da ake da ita a ƙasar nan.

Comments (0)
Add Comment