Jinkirin Bayar Da Rancen Kuɗin Makaranta Yana Ta’azzara Rayuwar Ɗalibai

Wasu ɗalibai da suka kammala karatu daga jami’o’in gwamnati sun bayyana takaicinsu kan yadda aka jinkirta biyan su rancen karatu daga hukumar NELFUND, inda suka ce kuɗin sun isa makarantu ne bayan sun kammala karatu kuma sun riga sun biya kuɗin rijista da kansu.

Waɗanda abin ya shafa sun bayyana a wata hira da jaridar The PUNCH cewa sun nemi rancen ne a lokacin da suke buƙatar biyan kuɗin rijista, amma sai suka nemi mafita ta daban yayin da kuɗin ba su iso da wuri ba.

“Na nemi rancen NELFUND lokacin da nake buƙatar kuɗi domin biyan kuɗin zangon ƙarshe, amma ban samu ba har sai da na biya da kaina, sannan bayan na kammala, sai na ga an biya makaranta kuɗin,” in ji wani dalibi.

WANI LABARIN: Har Yanzu Maƙiya Ci Gaban Ƙasa Na Yaƙi Da Matatar Dangote

Ya ƙara da cewa ya sanar da hukumar cewa ya kammala karatu, amma har yanzu ana turo masa da kuɗin gudanar da rayuwa na naira 20,000 kowane wata, yana mai cewa kuma dole zai mayar da su idan lokacin biyan bashin ya zo.

Hukumar ICPC ta fara bincike kan zargin cin hanci da almundahana da ke tattare da tsarin bayar da rancen, inda rahotanni suka nuna cewa daga cikin naira biliyan 100 da aka ware, naira biliyan 28.8 ne kaɗai ne suka isa hannun dalibai.

A cewar hukumar NOA da kuma ƙungiyar NANS, akwai shaidu da ke nuna cewa wasu makarantun da bankuna sun yi haɗin baki wajen jinkirta biyan kuɗin domin amfana da tsarin ta haramtacciyar hanya, ciki har da cire tsakanin naira 3,500 zuwa naira 30,000 daga kuɗaɗen da aka ba wa ɗaliban.

Shugaban ƙungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce suna sa ido kan lamarin kuma suna jiran sakamakon binciken, inda ya jaddada cewa dole ne a hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin wannan baƙin mugun hali.

Comments (0)
Add Comment