Jirgin Kasa Ya Yi Awon Gaba Da Motar Ma’aikata, Ya Kashe Mutum 6 A Lagos

Akalla ma’aikatan gwamnatin Jihar Lagos shida ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon awon gaba da wani jirgin kasa ya yi da wata motar bas a yankin Sogunle a jihar.

An gano cewa wata motar BRT da ke kai ma’aikatan gwamnatin jihar zuwa aiki, ta zo tsallaka layin dogo ne a lokacin da jirgin da ke tafiya ya makale.

Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Ibrahim Farinloye ya ce, an gano gawarwakin ma’aikata mata biyu na gwamnatin jihar wadanda suka mutu nan take, an kuma kwashe wadanda suka jikkata da dama zuwa asibiti, inda a can aka samu karin wadanda suka mutun.

“Bas din ma’aikatan gwamnatin jihar na kokarin tsallaka titin jirgin kasa a Sogunle yayin da jirgin da ya taso daga Abeokuta zuwa Lagos, ya makale,” inji Farinloye.

Jirkin KasaLagos
Comments (0)
Add Comment