JISEPA Ta Kama Lalatattun Kayayyakin Da Darajarsu Ta Haura Naira Miliyan 14 A Jigawa

Daga: Mika’il Tsoho, Dutse

Hukumar Kula da Lafiyar Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta bayyana cewa ta kama tare da lalata kayan abinci da sauran kayayyakin da ake sayarwa da suka lalace, ko wa’adin lafiyarsu ya ƙare, ko kuma suka gurɓace, da darajarsu ta kai Naira miliyan 14.4 a faɗin jihar.

Shugaban hukumar, Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani ga manema labarai kan kammala atisayen duba tsaftar muhalli da hukumar ta gudanar a duk ƙananan hukumomi 27 na jihar tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2025.

Ya ce atisayen ya shafi kasuwanni, kantuna da wuraren ajiya da cinikayya, inda aka mayar da hankali kan tabbatar da bin ƙa’idojin tsafta da kuma gano kayayyakin da ba su dace da amfani ba.

A cewarsa, aikin ya gudana ne ƙarƙashin doka, musamman Sashe na 5(1)(2) na Dokar Kariya ga Muhalli ta Jihar Jigawa ta 2009 da kuma Sashe na 125(1) na Dokar Kula da Lafiyar Jama’a ta 2024.

“An kama kayayyaki da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 14,447,650.00, waɗanda aka tabbatar da cewa wa’adin amfani da su ya ƙare, da waɗanda ba a adana su yadda ya kamata ba, ko kuma suna da haɗari ga lafiyar jama’a,” in ji shi.

WANI LABARIN: Ƴan Gudun Hijirar Cikin Gida A Najeriya Sun Haura Miliyan 8 – Rahoto

Ya bayyana cewa kafin a lalata waɗannan kayayyaki, an bi dukkan matakan doka da suka haɗa da tantancewa, rubuce-rubuce da samun izinin lalata su daga hukumomin da suka dace.

“Wannan mataki ba na hukunta kowa ba ne, sai dai yunƙurin kare lafiya da rayuwar jama’ar mu,” in ji Sabo, yana mai jaddada cewa kariya ga muhalli da lafiyar jama’a na daga cikin manyan ayyukan hukumar.

Ya ce JISEPA za ta ci gaba da aiki tare da ƙungiyoyin ƴan kasuwa, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki domin ganin an kiyaye doka da oda kan tsaftar muhalli da lafiyar jama’a.

A ƙarshe, ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da kayayyakin da suke saya, su goyi bayan hukumar wajen aiwatar da dokoki, su kuma riƙa ba da rahoto idan sun ga kaya da ke barazana ga lafiyar al’umma, yana mai cewa: “tare da haɗin kanmu, za mu gina Jigawa mafi tsafta da lafiya.”

Comments (0)
Add Comment