Sarkin Kano Mai Murabus, Alhaji Muhammadu Sunusi ya haɗu da shugabannin mulkin soja na Nijar a ƙasar ta Nijar ana tsaka da matsin lamba kan a dawo da Shugaba Mohammed Bazoum.
Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ne, ya haɗu da waɗanda suka yi juyin mulkin ne a yau Laraba bayan sojojin sun ƙi saurarar wakilan Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka, AU da na Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma, ECOWAS.
Faifen bidiyon da yake nuna haɗuwar Sarki Sunusi da masu juyin mulkin ya karaɗe kafafen sa da zumunta.
Idan za a iya tunawa jakadun ECOWAS, ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wadda Janar Abdulsalam Abubakar (Mai Ritaya) ke jagoranta ba su iya samun zaman lafiya da sojojin ba, inda sojojin suka ƙi da zama da su.
Amma a yau Laraba, faifan bidiyon Sarki Sunusi wanda ke a matsayin Khalifan Ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya wadda ke da mabiya masu ɗinbin yawa a Nijar ya zagaya duniya.
Khalifa Sunusi ya samu rakiyar Sarkin Damagaram, gari na uku a girma a Ƙasar Nijar domin ganawa da sojojin.
Jaridar DAILY TRUST ta gano cewar, Sarki Sunusi ya je Nijar ne da nufin samar da daidaito da kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa ta hanyar tattaunawa.