Kalubalen Noman Bana Bayan Ambaliyar Ruwa A Jigawa

Daga: Ahmed Ilallah

Ko shakka babu,shekrar da ta gabata na ta cikin shekarun da ambaliyar tayi muni a sassa da yawa na wannan kasa, manoman Jihar Jigawa na daga cikin wayanda suka fuskanci mummunan tasku a sanadiyar ambaliyar.

Jihar Jigawa na  daga cikin jahohin da suka fuskanci mummunan yanyi da tarun asarar amfanin gona da gonakai a dalililin wannan ambaliya.

Gonaki da amfanin noma, musamman ganaki fadama, da gonakin da suke da kusa da koguna. Manoma, wanda akasarin su kananan manoma ne, kuma talakawa, sun tafka muguwar asara a wannan dalilan.

Rashin kyakkyawan girbi a damminar da ta gabata dalilin ambaliyar ruwa, manoman sun shiga mawuyacin hali, wanda ba ta gona a ke ba, ta maganin yunwa da mawuyacin halin da aka shiga a ke.

Mummunan girbi da rashin kyakkyawan tsari daga gwamnati na rage radadi da cike gibi asarar da mutane suka yi, ya kara ta’azzara wannan matsaloli, ya kuma kara haifar da yunwa.

Daman harkar noma a Nijeriya yana cike da kalubale iri iri, da halin ko in kula da ga hukumomi. Har yanzu manoman mu da gonakan su irin na da ne, gadon iyaye da kakannu.

Duk cigaban da duniya tayi wajen cigaban noman zamani da dabaru na noma da sarrafawa da inganta gonakai don samun wadatuwar abinci, amma munanan jiya a yau.

Ko kadan bamu da daabarar kaucewa hadarin ambaliyar ruwa, tsarin taimako da rage radadi ga wanda suka fuskanci bala’in ambaliyar ruwa a gurbace take.

A yanzu dukkan alamu ya nuna kuratowar damina, amma shin manoman mu musammam masu noman bayi irin su shinkafa da dongogin su na da karfin komawa gona a yanzu? Shin su na da damar kara yawan amfanin da suke samarwa don tallafawa kasa.

Dadi da kari fa, a wasu yankunan na Jigawa ta Gabas, wanda muhimmai ne wajen samar da abinci su na fama da rashin tsaro, sanadiyar yawan arangama tsakanin makiyaya da manoma. Kananan hukumomi irin su Guri da Kiri Kasamma su na fama da wannan matsalolin a tsawan shekaru.

Ita ma wannan matsala fa har yanzu an gagara kawo karshen ta. Wannan matsala ba karamar hasara ta ke haifar wa ba, wajen hasarar kayan noma, wasu lokuta ma har da rayuka.

Magana ta gaskiya, ya zama dole, in har ana son dorewa da bunkasa noma bama a Jigawa kadai ba, ama Nijeriya, ya zama dole a waiwaici wannan matsaloli don bunkasa samar da abinci a wannan kasa.

A yanzu fa, inda komai na tafiya dai dai da tuni manoma sun cika jeji, jeji yayi kore da shinkafa yar rani, da watama ta soma zuwa gida, amma a wannan karon al’amuran ba kamar na baya ba.

Ya kamata duk masu ruwa da tsaki da fada a ji a sake duba lamarin wannan manoma namu na karkara, musamman wanda suka shiga wadannan hali don bunkasa noma da yakar yunwa. Allah ya bamu damina mai albarka.

Ahmad Ilallah ya rubuto ne daga Hadejia, Jigawa

alhajilallah@gmail.com

Ambaliyar RuwaJigawaNoma
Comments (0)
Add Comment