Kamfanin Dangote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 970 a Lita

Kamfanin Dangote Petroleum Refinery ya sanar da rage farashin man fetur (PMS) a tashar adana man sa zuwa Naira 970 a kan kowacce lita.

Wannan mataki, wanda aka sanar a ranar Lahadi, ya kasance ne domin nuna godiya ga ƴan Najeriya kan goyon bayan da suka bayar da kuma tallafa wa kasuwancin cikin gida. 

Anthony Chiejina, Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na kamfanin ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya nuna jajircewar kamfanin wajen tabbatar da isar da isasshen mai cikin gida. 

“Wannan shi ne hanyarmu ta nuna godiya ga ƴan Najeriya kan taimakonsu wajen tabbatar da wannan kamfanin ya zama gaskiya,” in ji sanarwar. 

Farashin na yanzu ya sauƙa daga na Naira 990 da aka sanar a farkon wannan watan. 

Chiejina ya ƙara da cewa: “Wannan mataki kuma yana nuna godiya ga gwamnati saboda tallafin da take bayarwa, tare da taimakawa wajen ƙarfafa kasuwancin cikin gida don jin daɗin mu duka. Za mu ci gaba da tabbatar da ingancin man fetur da ke dacewa da muhalli kuma mai ɗorewa.” 

Raguwar farashin zai bai wa ƴan kasuwa damar rage farashi da Naira 20 a kan kowace lita, wanda zai iya rage wa harkokin kasuwanci da mabuƙatan man nauyi. 

Matatar Dangote ta kuma tabbatar da jajircewarta wajen ƙara yawan samar da mai don biyan buƙatun cikin gida, wanda zai kawar da duk wani fargabar ƙarancin mai. 

Wannan sanarwar ta kasance wata kyakkyawar dama wajen magance damuwar hauhawar farashin mai, tare da ƙarfafa rawar matatar a fannin makamashi na Najeriya.

Comments (0)
Add Comment