Kano Ta Ɓullo Da Tsarin Bai Wa Ɗalibai Mata Tukuicin Naira 20,000 Don Bunƙasa Shigarsu Makarantu

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da fara bayar da tukuicin naira 20,000 ga ɗalibai mata da ke jihar domin bunƙasa sha’awarsu ta zuwa makaranta.

Gwamnan wanda ya sanar da ci gaban a jiya Lahadi lokacin da yake jawabin murnar zagayowar ranar ƴancin kan Najeriya a Filin Wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, ya ce, za a fara shirin da ƴanmata sama da 45,000.

Gwamnan ya kuma ce, gwamnatinsa zata sake dawo da tsarin motocin jigilar ɗalibai mata domin kai su da kuma ɗauko su daga makarantunsu.

Abba Kabir ya kuma ce, a ƙoƙarinsu na magance yawaitar waɗanda ba sazuwa makaranta da gararamba a kan tituna, gwamnati zata samar da ƙarin makarantun sikandire da na firamare a dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

KARIN LABARI: JERIN SUNAYE: Masu Degree Da Suka Samu Aikin Sa Kai Na J-Teach A Jigawa

Gwamnan ya kuma ce, yanzu haka ana kan gyaran makarantu a matakai, sannan kuma suna bayar da kayan makaranta, takalman ɗalibai, jakankunan ɗalibai, littatafan karatu da littattafan rubutu kyauta a makarantun firamare da ƙananan sikandire a matsayin mafari.

Ya kuma ce, an cimma matsaya kan samar da abinci guda a duk rana ga dukkan ɗaliban firamare da ke jihar.

Ya ƙara da cewar gwamnatinsa zata ɗauki nauyin ɗalibai 1001 masu shaidar karatu ta farko (first class) domin su yi karatun mastas a jami’o’in waje.

Abba Kabir YusufJihar Kano
Comments (0)
Add Comment